Algeria: An hallaka mutane biyu

Image caption Wurin da aka kai hari a baya

Wasu 'yan bindiga da ake alaƙanta wa da ƙungiyar Al Qaeda a kudu maso gabashin Mali sun kai hari kan wani bututun iskar gas, inda suka kashe masu gadi guda biyu da kuma jikkata wasu bakwai.

Masu gadin dai na cikin ɓangaren fararen hular da ke ɗauke da makamai da suke gadin bututun a yankin Bouria, inda mayakan Al Qaida suke da ƙarfi a yankin arewacin Afirka.

Harin wanda ya auku a ranar Lahadi na zuwa ne makonni biyu bayan da wasu 'yan bindigar dake da alaƙa da ƙungiyar ta Al Qaidan, suka sace ɗaruruwan ma'aikatan wata matatar iskar gas a kudancin Algeria, inda Talatin da bakwai a cikinsu suka mutu.

A baya dai Algeria tayi fama da tashin hankali dake da alaƙa da ƙungiyar Al Qaeda.