Borno: An 'kashe' mutane takwas

Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Borno na cewa an kashe wasu mutane su takwas a ƙauyen Gajiganna, inda aka yanka wasu daga cikinsu.

Koda yake rundunar tsaro ta JTF a jihar ta tabbatar da kai hari a ƙauyen, amma bata tabbatar da yawan waɗanda suka mutu a harin ba.

A makon jiya ne aka yanka wasu mutane biyar a Maiduguri, sai dai kawo yanzu babu wanda ya ɗau alhakin kai harin.

A baya dai ƙungiyar Ahlus sunna lil da'awati wal jihad wacce aka fi sani da Boko Haram ta yi ikirarin kai wasu hare-haren a birnin na Maiduguri dake fama da tashin hankali.