Brazil: Binciken gobarar da ta kashe mutane da dama

Image caption Gidan rawar da ta kama da wuta

Mahukunta a birnin Santa Maria da ke kudancin Brazil na binciken musababin gaborar da ta hallaka mutane 233 a yayinda mutane 120 su ka samu raunuka a wani gidan rawa.

Bincike zai maida hankali ne akan bayanan dake nuni da cewa an yi wasan wuta ne a dandalin da wasu mawaka ke kade-kade kuma mutane da dama sun kasa fice daga dakin saboda kofar gaggawa guda daya ce rak.

Kasar Brazil bata taba fuskantar abun tausayi irin wannan ba tun bayan farko shekarun alif dari tara da sittin.

Wannan al'amarin dai ya sanya al'ummar kasar zaman makoki.

Dalibai da dama ne wadanda shekarunsu basu wuce 19 zuwa 21 ne su ka rasu a jerin sunayen da gwamnati ta fitar na wadanda su ka rasa rayukansu.

Daya daga cikin wadanda ke da gidan rawan ya tabbatar da cewa suna kokarin sabonta lasisin kiyaye gobara ne na gidan da ya kare a bara a lokacin da ya gobarar ta auku.

Ya ce mutane da dama na tura mishi sakonin barazana ga rayuwarsa ta shafin Intanet.

A yayinda al'ummar kasar ke jimamin abun fa ya faru, ana ci gaba da tafka muhawara a Brazil kan yadda wadannan mutane suka rasa rayukansu.