Faransa na kokarin shiga Timbuktu

Ana ci gaba da samun rahotannin da ke karo da juna game da yunkurin da sojojin Faransa ke yi na kwato garin Timbuktu da ke arewacin Mali.

Har yanzu dai babu tabbaci ko Sojojin Faransa da na Mali sun shiga cikin garin.

Sai dai dubban mutane na ci gaba da bakukuwan murnar shiga sojoji cikin garin Gao a yayinda 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama su ka bar garin su ka shige cikin hamada.

wasu majiyoyi masu karfi sun ce sojojin Faransa sun kwace filin saukar jiragen sama na Timbuktu amma har yanzu dai babu tabbacin cewa sun samu shiga cikin garin.

Har yanzu dai ba'a samun wayar salula a garin abun da kuma ke kawo cikas wajen ganawa da mazauna garin domin sanin irin abubuwan da ke faruwa.

Faransa ma dai ya zuwa yanzu ta ki amincewa ko ta kai hare-haren jiragen sama a garin Kidal da ke kusa da iyakar kasar Algeria.

Amma duk da yake ana samu matsala wajen tabbatar da sahihancin rahotanin abubawa da ke faruwa a garin dubban mutane ne suka fito kan tituna a garin Gao na nuna farin cikinsu da ficewar da yan tawayen suka yi daga garin.

Wani mai magana da yawun sojin Faransa ya ce har yanzu dai akwai baban aiki a gaba, ganin cewa 'yan tawaye da dama ne su ka shige cikin farar hula.