Argentina da Iran za su hada guiwa

Image caption An kaiwa wata cibiya ta Yahudawa harin bomb din ne a shekarar 1994 a birnin Buenos Aires.

Kasashen Argentina da Iran sun ce zasu kafa wani kwamitin hadin guiwa da zai binciki harin bomb din da aka kaiwa wata cibiya ta Yahudawa a shekarar 1994 a birnin Buenos Aires.

Kwamitin dai zai kunshi alkalai bakwai ne masu zaman kansu wadanda kuma ba 'yan asalin kasashen biyu bane.

Wasu kotuna a kasar Argentina a baya sun zargi Iran da kai harin da yayi sanadiyar mutwar mutane tamanin da biyar

Iran dai ta musanta zargin.

Shugabar kasar Argentina, Cristina Fernandez, ta bayyana yarjejeniyar kafa kwamitin a matsayin wani babban abin tarihi.

To sai dai tilas ne sai Majalisun dokokin kasashen biyu sun amince da kafa wannan kwamitin kafa ya fara aiki.