Iran ta harba Biri sararin samaniya

Birin da Iran ta harba a Roka
Image caption Birin da Iran ta harba a Roka

Kasar Iran tace ta samu nasarar harba Biri sararin samaniya a cikin roka mai suna Pishgam, inda ya yi tafiyar kilomita 120 a sama.

Rokar dauke da birin ta dan yi shawagi a sama, kuma ta dawo lafiya, a cewar ma'aikatar tsaron kasar.

Gidan talabijin na Iran ya nuna hoton bidiyon birin, wanda aka daurawa damara a yayin da za a kaishi cikin Rokar.

Kasashen yamma na nuna damuwa game ayyukan Iran na sararin samaniya, inda suke ganin kasar na amfani da su ne domin shirya kai harin makamai masu linzami na dogon zango.

Kuma za a iya amfani da shirin wajen aika makaman kare dangi.

Sai dai Iran ta musanta shirin yin makaman kare dangi, inda ta sha nanata cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne.

A shekarar 2010, Iran ta samu nasarar harba bera da kunkuru da kuma tana zuwa sararin samaniya.

Amma yunkurin da ta yi na harba biri a shekarar 2011 bai yi nasara ba.

Haka kuma a shekarar 2010 ne, Shugaba Ahmadinejad ya sanar da cewa, kasarsa na da shirin aika mutum zuwa sararin samaniya a shekarar 2019.

A karon farko, Iran ta harba tauraron dan adam da ta kera a cikin gida zuwa sararin sama a shekarar 2009.