MEND: Gwamnati ta mayar da martani

Image caption Wata Kotu a kasar Afrika ta kudu ce ta samu Mista Okah da hannu a kitsa ta'adancin

Gwamnatin Najeriya ta bukaci 'yan kungiyar MEND da su kasance masu martaba doka maimakon daukan duk wani matakin da zai wargaza zaman lafiyar kasar.

Gwamnatin dai na maida martani ne ga wata barazanar da kungiyar ta yi cewar za ta kaddamar da hare-hare a kan manyan jami'ai da kuma wasu kadarorin gwamnati.

Kungiyar ta ce za ta yi hakan ne matukar aka aiwatar da hukunci a kan tsohon shugaban kungiyar, Mr Henry Okah.

Wata kotun a kasar Afirka ta kudu ce ta same shi da hannu a haren-haren bom da aka kai a watan Oktoban shekara ta 2010, lokacin bukin samun 'yancin Najeriya.

Mr. Labaran Maku, Ministan yadda labarai a Najeriya ya ce; "Henry Okah ba a Najeriya aka same shi da laifi ba, saboda haka banga dalilan da wasu ke kokarin tada zaune tsaya a cikin Najeriya."

"An gurfanar da shi ne a kasar Afrika ta kudu kuma an bi doka kuma lauyoyi sun wakilce shi".

Ministan ya ce duk wanda bai amince da hukunci da aka yiwa Mista Okah ba ya garzaya zuwa kotu.