Boko Haram: Jami'ai na zuba ido kan tsagaita wuta

Kanar Sambo Dasuki
Image caption Mai baiwa shugaban Najeriya shawara game da harkar tsaro, Kanar Sambo Dasuki

Shalkwatar tsaro ta Najeriya, ta ce za ta zuba ido ta gani, ko da gaske ne ikirarin da wani ya yi na cewa yana magana da yawun kungiyar jama'atu Ahlus Sunnah Lidda'awati wal jihad, game da tsagaita wuta.

A hirar da ya yi da 'yan jaridu da turanci a ranar Litinin, Abu Muhammad Ibn Abdulaziz ya ce, sun tsagaita bude wuta ne sakamakon tattaunawar da suka yi da gwamnatin jihar Borno.

Kuma in ji shi, ya samu izinin shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau kafin ya bada sanarwar, don haka ya yi kira ga 'ya'yan kungiyar da su dakatar da kai hare-hare a fadin kasar.

Ya kuma kara da cewa, sun tsagaita bude wutar ne saboda wahalhalu da yara da mata ke fuskanta, inda ya yi kira ga jami'an tsaro da su bada hadin kai.

Shi dai Abu Muhammad Ibn Abdul Aziz a baya sau biyu yana fitar da sanarwar cewa kungiyar a shirye take ta tattauna da gwamnati, amma kuma aka ci gaba da kai hare-hare.

Matsayin soji

A martanin da ya mayar game da sanarwar, babban hafsan sojojin Najeriya Admiral Ola Ibrahim ya shaida wa manema labarai cewa, ikirarin da Abu Muhammad ya yi, ba abu ne da za su fara aiki da shi nan take ba.

Za su jira har tsawon kimanin wata guda, idan ba a samu hare-haren bama-bamai ba, ko kashe-kashen jama'a da lalata masallatai ba, sannan ne za su yarda a fara tattaunawa.

Sai dai wasu dake bin al'amuran kungiyar ta Boko Haram sun ce, suna kaffa-kaffa da sanarwar, ganin cewa an kashe wasu mutane akalla takwas a ranar da aka bada sanarwar.

Haka kuma wata majiya dake kusa da kungiyar ta fitar da wata sanarwa dake cewa, shugabannin kungiyar ta Boko Haram sun ce ba za su ce komai ba game da ikirarin na Abu Muhammad Ibn Abdul Azeez, saboda da alamu 'yan Najeriya basa daukar darasi.

Ta kuma cigaba da cewa kungiyar za ta cigaba da yiwa 'yan jarida dariya, saboda abin da ta kira yaudarar su da ake yi cikin sauki.