Isra'ila ta ki halartar taron cin zarafin Bil adama

Benjamin Netanyahu
Image caption An soki Isra'ila ta kin halartar taro akan cin zarafin Bani adama

An soki kasar Isra'ila bayan da taki halartar taron Hukumar kare hakkin bil'adama ta majalisar dinkin duniya da akan yi akai-akai a birnin Geneva.

Mambobin hukumar da dama sun yi kakkausar suka ga abinda Israilan tayi, suna masu nuna cewa nazarin da kwamitin sulhun yake yi na duk kasashen duniya ne, kuma dukkan Kasashe su shiga ciki harda Syria da Koriya ta Arewa.

A yanzu Hukumar ta dage nazarin, inda aka shaida wa Isra'ilan cewa ana tsammanin ganin ta, domin ayi nazari kan batun cin zarafin bil'adama a kasar ta, zuwa karshen wannan shekarar.

A watan Mayun da ya gabata, Israila dai tayi ce ta dakatar da hulda da kwamitin, saboda a cewarta yana nuna mata son kai.

Karin bayani