Garanbawul ga dokar shige da fice a Amurka

Wasu fitattun 'yan Majalisar dattawan Amurka da suka fito daga jam'iyu daban daban sun gabatar da wasu muhimman shawarwari game da shirin yiwa tsarin shige da fice na kasar garanbawul.

Shawarwarin dai sun hada ne da daukar tsauraran matakan tsaro akan iyakoki da kuma duk wadanda aka samesu da daukar bakin haure aiki a kasar.

Sai dai a bangaren guda kuma, 'yan Majalisar dattawan sun bada shawarar da baiwa bakin haure su kimanin miliyan goma sha daya dake Amurkan takardar izinin zama 'yan kasa.

Sanata Charles Schumer dan Majalisar dattawa daga bangaren Jam'iyar Democrat, ya bayyana cewa sun cimma shawarwarin ne ba tare da la'akari da bambanci Jam'iya ba.

Ya ce; "A karon farko, mun gano cewa akwai hadari ta fuskar siyasa a nuna adawa da yiwa tsarin shige da fice na kasar garanbawul maimakon nuna goyon baya ga tsarin."

Idan an jima a yau ne kuma Shugaba Barrack Obama wanda yayi marhabin da shawarwarin da 'yan Majalisar dattawan suka gabatar zai bayyana sabon shirinsa na yi wa dokoki shige-da-fice na kasar garambawul.