Gwamnatin Najeriya ta bada kuɗin yaƙi da guba

Image caption Wurin hada-hadar ma'adinai a Zamfara

Gwamnatin Najeriya ta bada kuɗin da za a yi amfani da shi wajen aikin inganta muhallin wasu al'umomin da suka gurɓace, sakamakon ayukan hakar ma'adinai a jihar Zamfara.

Ƙungiyoyin dake rajin kare muhalli da hakkokin bil'ama sun dauki lokaci suna kira ga gwamnatin Najeriya data bada kudin, don ceton rayukan al'umomin, wadanda suka ce suna fuskantar mummunan hadari.

Tunda daga lokacin da matsalar ta ɓarke dai yara da dama ne suka mutu.

Tuni ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Humanr Rights Watch ta yabawa wannan mataki da gwamnatin ta ɗauka