Birtaniya za ta taimakawa Algeria ta fuskar tsaro

Mr Cameron a lokacin da ya sauka Algiers
Image caption Mr Cameron yana fatan taimakawa Algeria ta fuskar tsaro

Firayim ministan Birtaniya, David Cameron ya fara wata ziyarar aiki a Algeria, inda ya yi alkawarin yin aiki tare ta fuskar tsaro da ƙasashen yankin, sakamakon garkuwar da aka yi da mutane a ƙasar, abun da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan arba'in, shidda daga cikinsu 'yan Burtaniya.

Shugabannin tsaro da na leƙen asirin Birtaniya na tare da Mr Cameron a wannan ziyarar.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan inganta tsaro a matatun iskar gas kamar wacce aka kaiwa hari makonni biyu da suka wuce da kuma batun hana safarar makamai daga Libya.

Mr Cameron ya ce fatansa shi ne taimakawa Algeria ta kare kanta daga barazanar masu fafutukar da ake alaƙanta wa da ƙungiyar Al- qaeda.

Karin bayani