Masar ta nemi bashi daga Jamus

Image caption Shugabannin Masar da Jamus

Shugaban ƙasar Masar, Muhammad Morsi ya tashi zuwa Jamus a wani ƙoƙari na samun bashin da gwamnatinsa ke matukar bukata, duk da tashin hankalin da ake fama da shi a ƙasar.

Mutane biyu sun mutu a faɗa na baya-bayan nan a kusa da dandalin Tahrir.

Shugaba Morsi zai yi ƙoƙarin shawo kan shugabar Jamus Angela Markel, cewa ƙasarsa na mayar da hankali wurin karafafa tsarin demokuradiyya.

Wakilin BBC a Berlin ya ce, Masar na son Jamus ta yafe mata dala miliyan 300 da take binta.

Kuma tana tattaunawa a kan dala biliyan hudun da take nema daga IMF, domin farfaɗo da tattalin arziƙinta.

Sai dai Mista Morsi ya fasa zuwa birnin Paris daga Berlin ɗin.