Mrs Gifford ta yi kiran gaggauta hana amfani da bindiga a Amurka

Gabrielle Giffords da mijinta
Image caption Giffords ta ce lokaci ya yi da 'yan siyasa za su tashi tsaye

Tsohuwar 'yar Majalisar wakilan Amurka, wacce ta tsallake rijiya da baya, sakamakon harbin da aka yi ma ta a ka, shekaru biyu da suka wuce a jihar Arizona, ta bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawan ƙasar, domin kiran a gaggauta daukar matakin hana amfani da bindiga.

Gabrielle Giffords ta ce yara ƙanana da dama na mutuwa saboda haka lokaci ya yi da 'yan siyasa za su tashi tsaye.

Zaman jin bahasin shi ne na farko tun bayan mummunan kisan da aka yi wa ɗalibai a wata makaranta a birnin Connecticut a watan da ya gabata - abinda ya sake tayar da batun dokar taƙaita amfani da bindigogi a Amurka.

A kwanakin nan Mrs Giffords ta kafa wata ƙungiya da ke samar da kudi domin tunkarar karfin da masu sayar da bindigogi ke da shi a kan 'yan siyasa.

Karin bayani