Tukuicin dala 30,000 ga 'yan Najeriya

mikel obi
Image caption Mikel Obi da takwarorinsa na Najeriya sun sami garabasar daloli

Najeriya ta baiwa 'yan wasanta dala 30,000 kowannensu a matsayin tukuici saboda tsallakewa zuwa zagayen gab da na kusa da karshe a gasar cin kofin Afrika ta 2013.

"Muna baiwa kowanne dan wasa dala dubu 30 saboda nasarar da suka yi.

Kowanne ya karbi kudin tukuicinsa a ranar Laraba," kamar yadda Daraktan kula da wasanni na Hukumar Kwallon Najeriya NFF, Dr Muhammed Sanusi ya shaida wa BBC.

Tawagar Super Eagles ta tsallake ne bayan ta samu galaba a kan kasar Ethiopia wato Habasha da ci biyu da nema a wasan da suka buga ranar Talata a birnin Rustenburg na kasar Afrika ta Kudu.

Najeriya da Ivory Coast

Mai horar da 'yan wasan Najeriyar Stephen Keshi ya samu dala dubu sittin a yayin da mataimakansa suka samu dala dubu 45 kowannensu.

Dr Sunusi ya kara da cewar an cimma yarjejeniya tsakanin 'yan wasan da jami'an a kan cewar idan sun tsallake za a basu tukuici, idan kuma aka fitar dasu ba za a basu komai ba.

"Mun basu tukuici kamar sun samu nasara a wasanninsu uku, saboda da a ce an dokesu, ba za su samu komai ba", a cewarsa.

Najeriya ta tsallake zuwa zagaye na gaba, a yayin da aka fitar da Zambia daga cikin gasar saboda ta tashi babu ci tsakaninta da Burkina Faso a nata wasan.

Hakan na nufin Super Eagles din za su fuskanci Ivory Coast a zagayen gab da na kusa da karshe a ranar Lahadi.

Karin bayani