Faransa ta mika kayan tarihi ga Najeriya

Image caption Ba a dai fadi kiyasin kudin kayan ba amma an yi amannar cewa sun kai shekaru kusan dubu uku.

Gwamnatin Faransa ta mika wadansu sassake-sassake na 'yan asalin kabilar NOK ga gwamnatin Najeriya.

Jami'an hana fasa kwauri na Faransa ne suka kwace sassake-sassaken daga hannun wani dan kasar Faransar a filin saukar jiragen sama na Paris a shekara ta dubu biyu da goma.

Ba a dai fadi kiyasin kudin kayan ba amma an yi amannar cewa sun kai shekaru kusan dubu uku.

Ofishin jakadancin Faransa a Najeriya ne ya mika sassake-sassaken ga gwamnatin Najeriya.

Gwamnatin Faransa ta ce ta mika kayan tarihin ga Najeriya saboda yarjejeniyar da kasashen biyu suka sa hannu a kai na raya al'adun gargajiya.