Yanke hukunci kan malalar mai a Najeriya

Image caption Wannan ne karo na farko da ake gurfanar da kamfanin mai a Holland a kan gurbata muhalli

A yau ne wata kotu a kasar Holland za ta yanke hukunci kan karar da wasu manoma da masu kamun kifi a yankin Naija Delta na Najeriya suka shigar gabanta inda suke kalubalantar kamfanin hakar mai na Shell da gurbata musu muhalli.

Wata kungiyar dake fafutikar kare muhalli mai suna Friends of the Earth ce ta shigar da karar a madadin wasu 'yan Najeriyar inda suke neman a biyasu diyya na gurbata musu muhalli.

Su dai wadannan manoman sun yi zargin cewa malalar mai da bututan mai na kamfanin Shell yayi sanadiyar gurbata musu muhalli har ta kaiga basa iya ciyar da iyalansu.

To sai dai kamfanin Shell ya ce satar mai da kuma zagon kasa da wasu ke yi a bututan mai na kamfanin su suka haddasa gurbata muhalli inda kamfanin yace yana iyakacin kokarin na ganin ya tsaftace muhalli a yankin.