Kotu ta wanke Shell kan tuhume-tuhume

woman walking
Image caption Wata mace na tafiya kusa da bututun mai na kamfanin Shell a Utorogu dake Warri

Wata kotu a Netherlands ta yi watsi da hudu cikin tuhume-tuhume biyar da aka yi wa kamfanin mai na Shell game da malalar mai a Najeriya.

Sai dai ta samu reshen kamfanin man dake Najeriya da laifin gurbata muhalli a kara daya, inda ta umarci kamfanin ya biya wani manomi diyya.

Kamfanin na Shell ya ce, ya yi maraba da hukuncin, a shari'ar mai cike da tarihi.

Wasu manoma hudu ne 'yan Najeriya suka shigar da karar, tare da wata kungiyar kare muhalli ta Friends of the Earth, kuma sun ce hukuncin ya basu matukar mamaki.

Kodayake kungiyar ta yi murna da samun Shell da laifi a kan tuhuma daya da kotun ta yi, amma ta ce zasu daukaka kara saboda a cewarsu ba'a samar wa alkalan cikakakken bayanai ba game da lamarin.

A shekarar 2008 ne dai aka shigar da karar a kasar ta Netherlands, inda shalkwatar kamfanin na Shell take.

Wadanda suka shigar da karar sun bukaci kotun ta mayar musu da kudaden shigarsu da suka yi asara, sakamakon gurbatar muhalli da kuma na ruwa a yankin Niger - Delta.