Syria ta zargi Isra'ila da kai ma ta harin bam

Taswirar Syria
Image caption Taswirar Syria

Gwamnatin Syria ta ce jiragen yaƙin Isra'ila sun kai harin bam a kan wata cibiyar bincike ta soja dake Arewa maso Yammacin Damascus, babban birnin ƙasar.

Gidan talabijin ƙasar ta Syria, ya ce ma'aikatan cibiyar biyu sun hallaka, kuma wasu ƙarin biyar sun samu raunika a sanadiyyar harin, wanda aka kai da asubahin ranar Laraba.

Gidan talabijin ɗin ya kuma musanta rahotannin dake cewa jiragen yaƙin na Isra'ila sun kai harin ne a kan wani ayarin motocin soja na Syria dake kan hanyar su ta zuwa yankin kan iyaka da Lebanon.

Har ya zuwa yanzu dai, Isra'ila ba ta tabbatar da labarin kai harin ba.

Jami'an Isra'ila dai sun sha nuna damuwa cewa masu fafutika na ƙungiyar Hezbollah za su iya samun makamai daga Syria.