Rikicin Syria ya kai makura

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin kasar Syria, Lakhdar Brahimi, ya shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar cewa rikicin da ake yi a Syrian ya kai makura.

Mr Brahimi ya kara da cewa sannu a hankali ana ta ruguza kasar Syrian inda ya ce tilas mambobin kwamitin tsaro na Majalisar wadanda ya ce kawunansu a rabe yake su dauki mataki.

Wasu jami'an diplomassiya da su ka halarcin taron sirri da Lakdar Brahimi ya yi da kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya sun ce, jami'in ya shaidawa kwamitin yadda abubuwa su ka tabarbare a Syria.

Babban Jami'in ya shaidawa manema labarai cewa gwamnatin Syria da 'yan adawa na hada kai wajen durkusar da kasar a hankali a yayinda kumaya yi gargadin cewa rikicin na iya yaduwa zuwa wasu kasashe da ke yankin.

Ya ce dolene kwamitin ta kawar da ban-bance ban-bancen dake tsakaninta domin magance matsalar.

Har yanzu dai ba'a san matsayin Mr Brahimi ba game da rawar da Shugaban Syria, zai taka wajen kawo zaman lafiya a kasar.

Kasar Amurka dai da wasu kasashen yamma na nuna goyon baya ne ga bukatun 'yan adawar kasar wadanda ke neman shugaba Assad ya sauka kafin a fara tattaunawar zaman lafiya.

Kasar Rasha da China sun nace cewa ba zasu goyi bayan bukatar 'yan adawan ba a yayinda suka hau kujerar naki sau uku a lokacin da aka gabatar da kuduri a gaban kwamiti da kai neman a yiwa Syria matsin lamba domin kawo sauyi a gwamnatin kasar.

Mista Brahimi dai yana ta tattaunawa da Jami'an kasar Rasha da na Amurka, a kokarinsa na hada kan kasashen biyu domin cimma matsaya a kan Syria amma ya ci tura.

A kwanakin baya dai kasashen biyu sun rabtaba hannu a wani shiri da zai ba gwamnatin rikon kwarya a kasar cikakken iko amma, yarjejeniyar bata fayyace matsayin Mista Assad ba.

Mr Brahimi dai ya ce lallai sai a warware wannan sarkakiyar, domin sanin irin rawar da shugaba Assad zai taka.