Majalisar dinkin duniya ta gargadi Isra'ila

Benjamin Netanyahu
Image caption Shirin gina matsugunan Isra'ila na shan suka

Wani sabon rahoton majalisar dinkin duniya ya ce gina matsugunan 'yan kama wuri zauna da Israela ke yi a Zirin Gaza ya keta hakkin Palasdinawa.

Majalisar dinkin duniyar ta kuma yi kira ga Israela da ta dakatar da gine-ginen nan take, ta kuma janye 'yan kama wuri zauna daga yankunan Palasdinawa da ta mamaye.

Rahoton wanda wasu kwararrun majalisar dinkin duniya kan hakkin bil adama suka wallafa, ya ce matsugunan a fakaice suna kawar da Palasdinawa da ga yankunansu sannan suna janyo musu wariya da cin zarafi a kowacce rana.

Isra'ilan dai ta ce an nuna son rai a rahoton.

Karin bayani