Shirin hana acaba a wasu sassa na jihar Kaduna

  • 31 Janairu 2013
Alhaji Mukhtar Ramalan Yero
Image caption Jihohin Arewa da dama ne suka hana acaba bisa dalilan tsaro

Gwamnatin jihar Kaduna dake Arewacin Najeriya ta bayyana aniyar ta ta hana hayar babur a wasu ƙananan hukumomin jihar.

A jiya ne dai yayin wani taron manema labarai, gwamnatin jihar ta Kaduna ta bada sanarwar , tana mai cewa tuni ma'aikatar shari'a ta fara tsara wata doka da za ta haramta acaba a kananan hukumomin kaduna ta kudu da kaduna ta arewa da Zaria da Sabongari da kuma wasu sassa na Igabi da Chukun.

Sai dai jama'a na nuna rashin jin dadinsu da wannan shiri, suna masu cewa hanyar samun abincinsu ne zaa toshe, musamman ganin cewa gwamnatin ba ta yi ma su wani tanadi na azo- a- gani ba.

Da ma dai kwanan nan jihar Kano ta hana goyo a babur a wasu sassa na jahar don shawo kan abun da ta kira matsalolin hare-hare da akan ƙaddamar a kan babura.

Karin bayani