Jam'iyyun siyasar Masar sun yi tir da rikicin kasar

Rikicin Masar
Image caption Siyasar Masar na cikin rudani

Shugabannin manyan jam'iyyun siyasar kasar Masar sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya ta yin watsi da tashe-tashen hankula, a wani kokari na kawo karshen kwanakin da aka shafe ana fito na fito tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro.

Ya zuwa yanzu mutane fiye da hamsin ne su ka rasa rayukansu.

An sanya hannu a kan yarjejeniyar ne a karshen wani taro tsakanin manyan jami'an kungiyar 'yan uwa Musulmi ta shugaba Morsi da kuma shugabannin adawa.

Jami'ar Azhar ce ta hada bangarorin biyu, a wani mataki da ba kasafai take yi ba na tsoma baki a harkokin siyasa.

A baya dai 'yan adawar sun yi watsi da kiran da Shugaba Morsi ya yi musu na a tattauna.

Karin bayani