Syria ta tabbatar da kai mata hari

Shugaba Assad na Syria
Image caption Shugaba Bashar al-Assad na Syria

Syria ta tabbatar da cewa jiragen saman yakin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a cikin kasar ta, amma ta musanta cewa an kai harin ne a kan wani ayarin manyan motoci da ke dauke da makamai zuwa Lebanon.

Bayanin da kasar ta Syria ta bayar a hukumance yana kunshe ne a wata sanarwa da kafofin yada labarai na gwamnati suka watsa.

Sanarwar ta ce jiragen saman yakin na Isra'ila sun ratsa sararin samaniyar Syria da asubahin ranar Laraba daga Tsaunin Hermon da ke kudu suna tafiya kasa-kasa ta yadda na'urar radar mai hango jiragen sama ba ta iya hango su ba.

Ta kuma ce jiragen yakin sun yi ruwan bama-baman ne a kan abin da ta kira wata cibiyar bincike ta tsaro a Jamraya, arewa maso yammacin babban birnin kasar.

Harin, a cewarta ya lalata cibiyar da wani gini da ke kusa da ita, da wani wurin ajiye motoci, sannan ya hallaka ma’aikata biyu ya kuma jikkata wadansu ma’aikatan su biyar.

Musamman sanarwar ta musanta rahotannin kafofin yada labarai wadanda suka ambato jami'an tsaro da na diflomasiyya a yankin suna cewa jiragen na Isra'ila sun kai hari ne a kan wani ayarin manyan motoci dauke da makamai da ya nufi iyakar kasar da Lebanon.

Sanarwar ta Syria ta alakanta harin da rikicin da ake fama da shi yanzu haka a kasar.

A cewarta, wadanda ta kira ’yan ta’adda sun sha yunkurin kai hari a kan cibiyar a ’yan watannin nan ba tare da sun yi nasara ba a abin da gwamnatin ke ganin wani yunkuri ne wanda ke samun goyon bayan kasashen waje na karya lagon kasar ta yadda ba za ta iya kare kanta daga hare-haren Isra'ila ba.

Ta kuma ce harin na Isra'ila keta hurumin sararin samaniya da diyaucin kasar ce amma kuma ba zai sa ta karaya ba har ta daina mara baya ga kungiyoyin ’yan gwagwarmaya da Falasdinawa.

Karin bayani