An kai hari ofishin jakadancin Amurka a Turkiyya

Turkiyya
Image caption Akalla mutane biyu ne aka kashe a harin

Akalla mutane biyu ne suka mutu bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai a wajen ofishin jakadancin Amurka a birnin Ankara na kasar Turkiyya.

Jakadan Amurkar ya ce wani mai gadi da kuma wanda ake zargin shi ya kai harin sun mutu.

Kafofin yada labaran Turkiyya dai sun ce an kai harin ne yayin da wasu jama'a da dama suka yi layi a gaban ofishin jakadancin na Amurka don neman takardun izinin zuwa kasar.

Wani mutum guda ya samu rauni sannan fashewar bam din ya lalata gine-ginen da suke kusa da ginin ofishin jakadancin na Amurka, da ke Unguwar Cankaya inda a nan Ofisoshin jakadancin kasashe da dama suke.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari.

Muna bakin ciki

Jakadan Amurka da ke Turkiyya, Francis Ricciardone, ya ce wani mai gadin Ofishin jakadancin ya rasa ransa; ya kuma yi godiya ga hukumomin Turkiya bisa daukin da suka kai cikin gaggawa.

"Muna mika godiya ga gwamnatin Turkiyya da gwamnan Ankara da kuma 'yan sanda bisa irin daukin da suka kawo mana cikin gaggawa.

Alal hakika muna bakin cikin rashin da muka yi na mai gadin mu, wanda dan Turkiya ne," a cewarsa.

A 'yan shekarun nan dai, wasu haramtattun kungiyoyi da suka hada da na Kurdawa 'yan aware da kuma masu fafutikar Islama, sun kai hare-hare a kasar ta Turkiya, wadda mamba ce a kungiyar kwancen tsaro ta NATO.

Karin bayani