Ana taro a kan muradun karni a Liberia

Susilo Bambang Yudhoyono, Ellen Johnson Sirleaf, David Cameron
Image caption Susilo Bambang Yudhoyono, da Ellen Johnson Sirleaf, da David Cameron ne ke jagorantar taron

Mambobin wani kwamiti mai karfin gaske da Sakatare Janar na Majalisar Dinikn Duniya ya kafa don ya duba makomar muradun karni na majalisar ya kuma bayar da shawarwari yana ganawa a Monrovia, babban birnin kasar Liberia.

Taron na Monrovia a kan abin da zai biyo bayan muradun karnin na Majalisar Dinkin Duniya ya sa komai ya tsaya cak a birnin wanda har yanzu yake farfadowa daga yakin basasa, kasancewar an girke ’yan sanda da ’yan sandan farin kaya a muhimman wurare don tabbatar da bin doka da oda.

An hana ababen hawa da ma mambobin kungiyoyi masu zaman kansu zuwa kusa da dakin taron—wani sabon otal na ’yan Lebanon wanda aka kaddamar saboda ganawar da kuma saukar da baki.

Masu fafutkar dai sun sha alwashin taruwa ne a kofar shiga dakin taron dauke da kwalayen da ke nuna rashin jin dadinsu dangane da abin da suka kira gazawar gwamnatin Liberia ta yaki talauci.

Kamar yadda aka tsara, shugabannin taron—shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf, da shugaban kasar Indonesia, Susilo Bambang Yudhoyono, da kuma Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron—za su gana da sauran mambobin kwamitin su 20 ranar Juma'a a asirce.

Samun bayani a kan abin da taron ke da burin cimmawa ya yi matukar wahala; sai dai wani masanin tattalin arziki a kasar ta Liberia, wanda ke sakatariyar taron, Sam Jackson, ya yiwa BBC takaitaccen bayani:

“Manufar wannan taro ita ce samar da tushen sauye-sauyen tattalin arziki; kuma wajibi ne sauye-sauyen su ginu a kan maudu'ai uku—ci gaban da ya kunshi ko wanne bangare, da hadin kan al'umma, da kuma kiyaye muhalli.

“Za kuma a fitar da sanarwar bayan taro wacce za ta shata hanyoyin ci gaban kasashen duniya bayan shekara ta 2015”.

Sai dai kuma Liberia na cikin kasashen da ke shugabntar taron ne duk da cewa, kamar sauran kasashen Afirka, ba ta kama hanyar cimma muradun karnin na Majalisar Dinkin Duniya guda takwas ba.

Karin bayani