Najeriya tayi galaba akan Ivory Coast

Wasu 'yan wasan Najeriya
Image caption Wasu 'yan wasan Najeriya

Najeriya ta doke Ivory Coast da ci biyu da daya a wasan dab da kusa da na karshe da kungiyoyin biyu suka buga a gasar cin kofin kasashen Afrika da ake yi a kasar Afrika ta kudu.

A yanzu haka dai Najeriya za ta hadu ne da kasar Mali wadda ta doke mai masaukin baki Afrika ta kudu.

Sunday Mba ne ya zura kwallon da ya ba Najeriya nasara a minti na 78 a wasan.

Emmanuel Emenike ne ya fara zura kwallon farko a ragar Ivory Coast tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, ana dawowa ne kuma Cheik Tiote ya fanshewa Ivory Coast.

Karin bayani