An kashe akalla sojoji 13 da wasu fararen hula a Pakistan

Pakistan
Image caption 'Yan Taliban sun kashe sojoji da farar hula a Pakistan

'Yan sanda a Pakistan sun ce akalla sojoji goma sha ukku da fararen hula goma sun rasa rayukansu a wani hari da aka kaiwa sojojin a wani wurin binciken ababen hawa a Khyber Pakhtunkhwa dake kusa da iyaka da Afghanistan.

'Yan tawaye kimanin talatin ne su ka afkawa wurin binciken wanda ke kusa da kofar shiga wani rukunin gidajen gwamnati.

'Yan sanda sun ce an dauki tsawon sa'oi ukku su na musayar wuta da 'yan tawayen.

Sun ce fararen hular da suka rasu wadanda su ka hada da mata shidda da kananan yara hudu, sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da wani makamin roka da 'yan tawayen su ka harba ya yi kaca- kaca da gidan da suke ciki.

'Yan Taliban na kasar Pakistan sun ce sune suka kai harin a matsayin ramuwar gayya na kwamandojin su biyu da aka kashe kwanannan a wani harin jirgi mara matuki.

Karin bayani