Iran ta yi maraba da tattaunar shirin Nukiliya da Amurka

Mahmoud Ahmadinejad
Image caption Ana shirin tattaunawar nukiliyar Iran

Ministan hulda da kasashen wajen Iran, Ali Akbar Salehi ya nuna karfin gwiwa dangane da wani sabon zagayen na tattaunawa akan samo hanyoyin diplomasiyya na warware rikicin nukiliyar Iran din.

Sai dai kuma jawabinsa bai bai nuna cewar ko akwai alamun za'a samu wani sabon cigaba ba a kokarin da ake na sasanta tsakanin Iran da wasu kasashen duniya dake nuna damuwa akan shirin nukiliyar Iran.

Yayin da yake jawabi cikin harshen Turanci, Ali Akbar Salehi ya nuna alamun neman sasantawa, amma yana tauna tsakuwa, inda yace, Iran tana da muhimmanci sosai a yankin gabas ta tsakiya, kuma ya kara da cewa, Iran ba 'yar amshin shatar kowacce babbar kasa ba ce.

Ministan hulda da kasashen wajen Iran din ya kuma yi marhabun da matsayin Amurka akan batun, inda yace, ya gamsu da kalaman mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden wanda yace, Amurka tana so ne a warware batun nukiliyar Iran ta hanyar tattaunawa.

Sai dai kuma yace, duk da hakan dole ne Amurka ta shiga cikin tattaunawa akan wannan batu da kyakayawar niyya.

Amma kuma ministan hulda da kasashen wajen Iran din ya dage cewa, kasar sa tana da 'yan cin yin shirinta na nukiliya.

Ali Akbar Salehi ya yi watsi da sukan da ake yiwa Iran dangane da rawar da take takawa a batun tashin hankalin dake gudana a Syria, yana mai cewa, 'yan kasar ta Syria ne kadai keda 'yan cin samowa kasarsu makoma.

Karin bayani