Tattaunawa ta yi armashi! Inji Karzai

Shugabannin kasashen Afghanistan da Pakistan - Hamid Karzai da Asif Ali Zardari - sun ce za su yi kokarin ganin sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya cikin watanni shida.

A wani taro da Burtaniya ta dauki bakunci, Fira minista David Cameron ya ce kasashen biyu na hada kai sosai.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan hanyoyin da za a bi don tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasashen Pakistan da Afghanistan.

Mr Karzai ya ce yayi murna ganin yadda suka samu ci gaba a yau.

Ya ce ya amince da jawabin Fira minista kan shirin samar da zaman lafiya da sauran al'amuran hulda tsakaninsu da Pakistan.

Shugabannin biyu sun ce sun amince da kafa ofis a birnin Doha na kasar Qatar, domin ganawa tsakanin Taliban da jami'an Afghanistan.