An ƙaddamar da sabon jagoran cocin Anglican

Image caption Justin Welby, jagoran cocin Anglican

Tsohon Bishop ɗin garin Durham a Biritaniya, Justin Welby, zai zama sabon jagoran Cocin Angalika na duniya, wato Archbishop na Canterbury na ɗari da biyar.

An yi bukin ne a wani taron addu'a da aka yi a Cocin St Paul Cathedral a yau a nan London.

Hakan ne bisa dokar cocin, zai tabbatar da zaben da hukumar zaɓen cocin ta yi masa.

Bishop Welby zai maye gurbin Dr Rowan Williams ne, wanda ya sauka a karshen watan Disamban da ya wuce, inda shi kuma zai je ya zama Shugaban Kwalejin Magdalene a Cambridge.

Cocin na Anglican dai yana da mabiya da dama a duniya.