An bankaɗo badaƙala a wasan ƙwallon ƙafa

Image caption Tutar hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya

Hukumar 'yan sandan Tarayyar Turai ta ce ta bankaɗo shaidun da ke nuna cewa ana sayar da wasannin ƙwallon ƙafa da dama a Turai da ma sauran sassan duniya.

Hukumar ta Europol, ta ce wani bincike da ta gudanar tare da 'yan sandan wasu ƙasashen, ya gano cewa an haɗa baki wurin sayar da wasanni kusan ɗari huɗu a Turai da wasu ɗari uku a Afrika da Asia da kuma Latin Amurka.

Kuma sun hada da wasannin gasar cin kofin duniya da na share fagen gasar cin kofin kasashen Turai.

Masu binciken sun ce wasu gungun mutane ne ke gudanar da harkar, waɗanda ke zaune ne a ƙasar Singapore tare da haɗin gwiwar miyagun mutane a Turai.