Mata a India na fargaba

Saurayin budurwar nan da wasu gungun mutane suka yi wa fyade a India, ya bayar da shaida kan lamarin wanda yayi sanadiyyar mutuwarta.

Saurayin wanda aka nakada wa duka a lokacin fyaden da aka yi a motar Bus, ya iso kutun ne a keken guragu.

Ana gudanar da shari'ar ne a asirce a birnin Delhi.

An kuma kawo motar Bus din da ake zaton an aikata ta'asar a ciki a gaban kotun.

Kavita Sharma, mamba a kungiyar kare hakkin mata ta All India Women Association, ta ce akwai bukatar daukar tsauraran matakai.

Inda tace ya kamata a samar da dokar da za ta kare mata, ta yadda duk wanda ke son aikata miyagun laifuka sai ya yi tunani tukunna kafin ya yi.

Duka mutane biyar din sun musanta tuhumar aikata fyade da kisan kai. Za a yi wa mutum na shida shari'a a kotun yara kanana.

Karin bayani