Za a tattauna makomar Mali a Brussels

Sojojin kasashen waje a Mali
Image caption Sojojin kasashen waje a Mali

Majalisar Dinkin Duniya da tarayyar Turai da kuma jami'an Afrika, za su tattauna game da yin sabon zabe a Mali, a wannan shekarar.

Taron na Brussels, zai kuma tattauna game da batun tsaro da na agaji, biyo bayan juyin mulkin sojin da aka samu a kasar bara, da kuma yakin da ake yi da masu fafutukar Islama a halin yanzu.

Dakarun Faransa da na Mali sun kori kungiyoyin 'yan fafutukar da ake alakantawa da kungiyar AlQaida, daga arewacin kasar da suka kwace.

Amurka da Faransa na son dakarun Afirka su karbi dakarun Faransa a Mali.

Masu aiko da rahotanni sun ce nasarar da dakarun da Faransa ke jagoranta ke samu cikin gaggawa, ya sa hankalin kasashen duniya ya karkata wajen tabbatar da zaman lafiya mai dore wa a Mali.