Shugaba Obama ya ja kunnen 'yan Kasar Kenya

Barack Obama
Image caption Barack Obama ya nemi 'yan Kenya su guji rikicin zabe

Shugaban Amurka Barack Obama ya aike da wani sakon bidiyo a shafin internet na You Tube ga jama'ar kasar Kenya - wato mahaifar babansa - inda nemi su gujewa tashe-tashen hankula a zaben kasa baki dayan da za a gudanar watan gobe.

Sakon nasa ya fara ne da gaisuwa a harshen Swahili.

Yace 'wajibi ne 'yan Kenya su sasanta rigin-riginmunsu a kotuna ba wai ta hanyar fada ba, mafi muhimmanci kuma, shi ne wajibi su hada hannu tare kafin zaben da kuma bayansa, wurin gina kasarsu'.

Mr Obama ya ce zaben wata dama ga 'yan Kenya su nana cewa su ba 'ya'yan wata kabila ba ne, illa dai mutane ne kawai masu alfahari da kasarsu baki daya.

Zaben shugaba kasar da aka gudanar a shekara ta 2007, ya rikide zuwa tashin hankali inda aka kashe fiye da mutane dubu daya.

Karin bayani