Amurka za ta kai karar Standard & Poors

Image caption Shugaba Barack Obama

Kamfanin da ke auna karfin iya biyan bashin kasashe, Standard and Poor's, ya ce Amurka na shirin gurfanar da shi a gaban kuliya a kan zargin cewa a shekarar 2007 ya yi kuskuren rage darajar takardun lamunin gidajen kasar.

Lamarin ya yi sanadiyar karya darajar takardun.

Ya kara da cewa babu wadansu sahihan alkaluma da Amurka za ta fitar wadanda za su nuna cewa ya yi kuskure wajen gudanar da aikinsa.

Wannan shi ne karon farko da wata kasa za ta shigar da kara a kan wani kamfanin auna karfin iya biyan bashin kasashe, wanda ya bullo bayan matsalar koma bayan tattalin arzikin da aka fuskanta a kasashen duniya.

A lokuta da dama kamfanonin na yin kuskure

Tun a shekarar 2007, ana ta tambaya game da irin rawar da kamfanonin auna karfin iya biyan bashin kasashe suka taka wajen haddasa matsaloli a fannin samar da gidaje.

Babban aikin kamfanonin shi ne sanya idanu a cibiyiyon kudi; su rika auna karfin iya biyan bashin kamfanoni da ma gwamnatoci domin masu zuba jari su san inda za su sanya kudadensu ba tare da fuskantar matsaloli da dama ba.

A lokuta da dama sukan karfafa gwiwar mutane don yin mu'amala da wani kamfani ko wata cibiyar kudi amma daga bisani akan samu sabanin, lamarin da kan yi sanadiyar fadawa rikicin tattalin arziki.

Karin bayani