'Faransa ta kashe daruruwan 'yan tawaye a Mali'

Image caption Jean-Yves Le Drian yana gaisawa da wani soja

Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya ce dakarun sojin kasashen duniya karkashin jagorancin kasarsa sun kashe daruruwan 'yan tawaye tun lokacin da suka fara kai farmakin soji a Mali a watan jiya.

Da yake magana da wani gidan talbijin na Faransa, Mista Le Drian, ya kara da cewa an yi matukar karya lagon 'yan tawayen.

Ya ce an kashe masu kaifin kishin Islama ne ko dai ta sama suna cikin motoci dauke da kayayyakinsu; ko kuma ta kasa, a fafatawar da suka yi a garin Konna, a farkon yakin, ko kuwa a garin Gao.

Masu sharhi a Faransa sun ce ba za a gane irin nasarar da kasar ta yi kan masu tayar da kayar bayan ba sai an yi la'akari cewa da fari an kiyasta 'yan tawayen za su kai 3000.

A nata bangaren, Faransa ta rasa soji daya, wanda ya mutu yayin wani hari da aka kai a jirgi mai saukar ungulu a farkon fara yakin.

Ma'aikatar tsaron ta ce adadin sojojin Mali da aka ritsa da su a yakin ba shi da yawa.

Karin bayani