'Ana gwabza fada na hakika a Mali'

Mali
Image caption Ana gwabza fada na hakika a Mali

Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian, ya ce a yanzu ana gwabza yaki na hakika a kasar Mali, bayan da aka bada rahotannin sabon tashin hankali a arewacin kasar.

Ya ce dakarun Faransa sun fatattaki wasu gungun mayaka ranar Talata a wajen garin Gao.

Wakilin BBC a Gao ya ce mayakan 'yan tawaye na da nisan kilomita tamanin ne kawai daga garin, kuma sun bar ababen fashewa a yankunan.

Kwanaki goma da suka gabata ne dakarun da Faransa ke wa jagoranci suka kwace Gao daga hannun 'yan tawaye.

A waje daya kuma Faransa ta yi kira ga Kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya da ya maye gurbin rundunar sojin kasashen Afrika da ke yakar 'yan tawaye a Mali, da wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar, akalla nan da watan Afrilu.

Sannan ta yi kiran a gaggauta tura masu sa ido na kungiyoyin kare hakkin bil'adama.

Karin bayani