Ana cire mahaifar dubban mata a India

Image caption Matan India

A kasar India, bara-gurbin likitoci na cire mahaifar dubban mata a yayin da suke yi musu tiyata domin su rika samun kudi.

Wannan lamari ya fi faruwa ne a asibitoci masu zaman kan su inda likitoci kan shaidawa matan cewa dole ne a cire musu mahaifar idan ba haka ba su kamu da cutar daji.

Wadansu matan da BBC ta tattauna da su sun ce sukan biya kimanin dala 200 domin a cire musu mahaifa.

Gwamnatin kasar ta ce an samu karuwar asibitoci masu zaman kan su ne sanadiyar rashin samun cikakkiyar kulawa daga asibitocin gwamnati.

An bukaci sanya idanu a kan asibitoci

Matan da ke tsakanin shekaru 20 zuwa 30 sun fi kasadar fuskantar wannan lamari, kuma sun ce likitoci na shaida musu bukatar cire musu mahaifar da zarar sun je asibitocin, ba tare da ba su wani zabi ba.

Ministan bunkasa yankunan karkara na kasar, Jairam Ramesh, ya ce asibitocin gwamnati sun gaza aiwatar da ayyukansu.

Masu fafutikar kare hakkin mata sun bukaci gwamnati ta rika sanya idanu sosai a kan irin wadannan asibitoci domin a tabbatar cewa ba su ci gaba da yaudarar mata ba, musamman wadanda ke fitowa daga karkara.

Karin bayani