Jiragen yakin Amurka na da sansani a Saudiyya

Jirgin yakin Amurka
Image caption Daga sansanin ne aka tashi jirgin da ya kashe Anwar al-Awlaki

Hukumar leken asiri ta Amurka CIA, ta shafe shekaru biyu ta na gudanar da wani sansani na jiragen yaki masu sarrafa kansu a kasar Saudi Arabia.

Kafafen yada labarai a Amurka sun san da zaman sansanin amma basu bayar da labari ba sai yanzu.

An kafa sansanin ne domin farautar 'yan kungiyar AlQaeda a kasar Yemen - daga sansanin ne aka tashi jirgin da ya kashe Anwar al-Awlaki a kasar ta Yemen a shekara ta 2011.

Shi dai haifaffen Amurka ne wanda ake wa kallon jagoran AlQaeda a kasashen Larabawa.

Kawo yanzu dai ba a bayyana inda sansanin yake ba.

Kungiyoyin masu fafutukar Islama da dama sun dade su na sukar gwamnatin Saudiyya kan alakar da take da ita ta kut-da-kut da Amurka.

Karin bayani