Khamenei ya yi watsi da tattaunawa da Amurka

Ayatollah Ali Khamenei
Image caption Ayatollah Ali Khamenei yace tattaunawa da Amurka ba zai waraware komai ba

Jagoran addinin Iran, Ayatollah Khamenei ya yi watsi da tayin tattaunawa ta keke-da-keke da Amurka ta yi game da shirin nukiliyar kasar.

A wani jawabin da ya yi wanda aka sanya a shafin intanet, Ayatollah Ali Khamenei ya ce Amurka na yin fuska biyu game da batun tattaunawar.

A ranar Asabar din da ta gabata ne , mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden ya yi tayin tattaunawar gaba-da-gaba da Iran, baya ga tattaunawar da ake shirin yi na kasa da kasa nan gaba a watan Fabrairun da ake ciki.

Kodayake ministan harkokin wajen Iran, Ali Akhbar Salehi ya yi maraba da tattaunawar, amma ya ce hakan abin dubawa ne, idan har Amurka na da kyakkyawar niyya.

Sai dai a ranar Larabar da ta wuce ne, Amurkar ta fadada takunkumin da ta sanya wa Iran, domin tsaurara hanyoyin kashe kudinta.

Masu sukar Iran dai na zargin kasar na shirin ne domin kera makaman nukiliya, abin da kasar ke musanta wa.

Kasashe biyar dake da kujerun dundundun a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da kuma Jamus sun sha yin tattaunawa game da batun a shekarun da suka gabata.

Sai dai Iran na gindaya sharadin janye takunkumin da aka kakaba mata, idan ana so ta yi wani abu game da shirinta na nukiliya, yayin da kasashen yamma kuma ke kekasa kasa.

A ranar 26 ga wannan watan ne aka shirya yin wata tattaunawar a Kazakhstan.

Karin bayani