Mata a Maiduguri sun yi bore kan mazajensu

Tasirar birnin Maiduguri
Image caption Jihar Borno ta shafe sama da shekaru uku tana fama da tashin hankali

Rahotanni daga Maiduguri a Najeriya na cewa, daruruwan mutane akasarinsu mata, sun yi cincirindo domin jiran mazajensu da suka ce JTF za ta sake.

Matan sun yi dandazo ne a dandalin Ramat dake tsakiyar birnin, domin jiran 'yan uwansu da ake tsare da su a barikokin soji dake garin.

Sai dai daga bisani matan da dama sun bar harabar dandalin, inda suka bazu kan titunan birnin suka yi zanga-zanga, bayan sun fahimci babu alamun sakin mazajen nasu da kuma 'yan uwansu maza.

Amma, Rundunar hadin gwiwar samar da tsaro ta JTF a jahar, ta ce, babu kanshin gaskiya game da yi musu alkawarin sakin mutanen.

Mutane da dama ne ake tsare da su a Maidugurin, sakamakon matsalar tsaro da ake fama da ita, game da rikicin kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.