Kungiyoyi sun damu kan zaman dakarun Faransa a Nijar

Kamfanin uranium a Nijar
Image caption Kamfanin uranium a Nijar

A jamhuriyar Nijar ana cigaba da cece-ku-ce game da zaman sojojin kasar Faransa dake kare wuraren hakar uranium na kamfanin Areva a Arlit dake Arewacin kasar.

A jahar Damagaram hadin gwiwar kungiyoyin farar hula, sun fitar da wata sanarwa inda suke nuna damuwa game da wannan batu.

Shugaba Muhamadou Issoufou ne ya shaida wa wasu kafofin yada labaran Faransa cewa, Faransa ta kawo dakaru na musamman domin kare kamfanonin hako uranium a jihar Agdez dake arewacin kasar.

Sai dai wasu na ganin, hakan wata kofa ce da Nijar ta bayar, na salwantar da ikonta na kasa mai cin gashin kanta, abin da gwamnatin ta musanta.