Fatawar kashe shugabannin adawar Masar

Mahukunta a kasar Masar sun ce za a girke 'yan sanda a wajen gidajen shugabannin 'yan adawar kasar, bayan da wani malamin addini ya bayar da fatawar a kashe su.

Malamin Mahmud Shaaban, ya bayar da fatawar ne a wani gidan talabijin.

Daga cikin sunayen 'yan adawar da malamin ya ambata har da tsohon shugaban hukumar kula da makamashi ta duniya Mohamed ElBaradei da kuma Hamdeen Sabahi.

Sai dai duka shugabannin addini da ma 'yan ba ruwanmu da addinin, sun yi watsi da fatawar, yayin da Fira ministan kasar Hisham Qandil, ya ce ana duba yiwuwar daukar matakan shari'a kan duk wanda ke bayar da fatawar da ke kiran ayi tashin hankali.