'Don dole muke amfani da jirgi mara matuki'

John Brennan
Image caption John Brennan ya kare matakin kai hari da jirgin sama mara matuki

Mutumin da Shugaba Obama ke so ya dare kujerar shugaban Hukumar Leken Asiri ta CIA ya kare matakin da Amurka ke dauka mai cike da cece-ku-ce na amfani da jirgin saman yaki mara matuki wajen kai hare-hare.

Da yake amsa tambayoyi a gaban kwamitin da ke kula da al'amuran leken asiri na Majalisar Dattawan Amurka, John Brennan ya ce dole ce ta sa ake amfani da irin wadannan jirage.

Mista Brennan, wanda yanzu haka shi ne mai baiwa Shugaba Obama shawara a kan harkar yaki da ta'addanci, ya yi kaurin suna saboda rawar da ya taka a dabarun da ke janyo ce-ce-ku-ce wadanda hukumar ta CIA ke amfani da su na tatsar bayanai daga mutanen da ake zargi.

Ya kuma yi kaurin suna wajen karfafa amfani da jirgin saman yakin mara matuki don kai hari a kan mayakan sa-kai.

Jim kadan bayan fara zaman kwamitin wanda zai tabbatar masa da mukamin ko akasin haka, wadansu masu zanga-zangar nuna adawa da amfani da jiragen marasa matuki sun tilasta dakatar da sauraren bahasin na dan wani lokaci.

Sai dai kuma daga bisani Mista Brennan ya ce wadansu daga cikin al'ummar Amurka ba su fahimci wajibcin amfani da jiragen ba:

A cewarsa, “Ina ganin wadansu daga cikin Amurkawa suna da mummunar fahimta, wadanda suka yi amanna cewa muna amfani da wadannan hare-haren ne a kan ’yan ta'adda saboda wadansu laifuffuka da suka aikata a baya: sam ba haka al'amarin ya ke ba”.

Ya kara da cewa, “Muna kai wadannan hare-hare ne kawai saboda mun kai makura; ba mu da wani zabi in muna so mu kare rayukan jama'a daga barazana. Na tabbata wadannan mutanen ba su fahimci wahalar da muke sha ba don tabbatar da cewa hare-haren ba su shafi mutanen da ba su ji ba ba su gani ba”.

Tun a farkon jawabinsa, Mista Brennan ya ce ba a taba shiga wani yanayi na tsananin bukatar bayanan sirri kamar yanzu ba.

Karin bayani