Badakalar sayar da naman doki ta yadu a Turai

Abincin lasasgne na kamfanin Findus
Image caption Daya daga cikin nau'ukan abincin da aka sa naman doki—lasasgne na kamfanin Findus

Badakalar sayar da naman doki da sunan jan nama a Birtaniya ta yadu zuwa wadansu kasashen Turai, inda aka kwashe naman da kamfanin abinci na Findus ke sarrafawa daga kantuna a Faransa da Sweden.

A yanzu haka dai hankali ya karkata ne kan kamfanin Comigel.

Kamfanin na Comigel mai samar da abincin gwangwani a Faransa, wanda kuma ke rarraba naman da kamfanin Findus ke sarrafawa, ya ce ya gano kamfanin da ke sarrafa gurbataccen naman.

Ma'aikatar Ayyukan Gona ta kasar Faransa ta bi sahun gwamnatin Birtaniya wajen nuna damuwa da yadda aka sayarwa mutane naman doki, tana mai cewa za ta gudanar da bincike kan yiwuwar aikata mummunan laifi.

A birtaniya, gwamnati ta kira wani taron gaggawa da jami’an kula da ingancin abinci, da masu sarrafa abinci da kuma masu sayarwa don duba hanyoyin da za a bi don tsaurara ka’idojin sayar da abincin.

Wakilin BBC ya ce tun a shekarar 2010 farashin shanu ya ke tashin gwauron zabi a Turai; kuma fadi tashin da masu sayar da naman sa ke yi na ganin sun sayar da naman da suka saba sayarwa a kan farashin da suka saba, shi ya sa naman doki ya samu kasuwa.

Karin bayani