Zabukan Kenya: Juma'ar da za ta yi kyau...

Uhuru Kenyatta
Image caption Uhuru Kenyatta yana barin kotun duniya dake Hague a shekarar 2011

Makwanni kadan kafin al'ummar Kenya su fita don kada kuri'a, daya daga cikin ’yan takarar shugaban kasar da Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya ke tuhuma ya yi kira da a dage sauraren shari'arsa a birnin Hague.

Uhuru Kenyatta—wanda da ne ga shugaban kasar ta Kenya na farko, Jomo Kenyatta—daya ne daga cikin fitattun mutanen da ake tuhuma da aikata laifin cin zarafin bil-Adama yayin tashin-tashinar da ta biyo bayan zaben da aka gudanar shekaru biyar da suka wuce, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu daya da dari uku, dubu dari biyar kuma suka rasa muhallinsu.

Sai dai kuma Mista Kenyatta zai yi wata sabuwar fafutuka ta wanke kansa a kotun ta duniya wata guda bayan zaben.

Ko da yake yana kewaye da masu tsaron lafiyarsa, Uhuru Kenyatta ya amince ya yi magana da BBC.

Da aka tambaye shi ko yana ganin ci gaba da yakin neman zabensa zai zama alheri ga Kenya, sai ya ce:

“Babu shakka alheri ne ga Kenya; wannan shi ne dimokuradiyya—a kyale mutane si yiwa kansu zabi”.

Da aka tambaye shi ko ba ya ganin cewa kamata ya yi ya fara wanke kansa daga tuhuma tukuna, sai ya ce ai babu alaka tsakanin batutuwan biyu.

Dan takarar da ke tafiya kai-da-kai da Mista Kenyatta shi ne Raila Odinga, mutumin da ke jin cewa an yi masa fashin nasarar da ya yi a zaben da ya gabata.

Magoya bayansa sun gudanar da mummunar zanga-zanga lokacin da ya sha kaye; yanzu kuwa zarginsa ake yi da cin amanar abokan siyasarsa a Hague.

Sai dai a cewarsa, “Sam sam, babu kamshin gaskiya a wannan magana. Kamar yadda kuka sani, an kafa hukuma don ta binciki dalilan da suka haddasa tashin-tashinar bayan zaben; kuma sakamakon shawarwarin da ta bayar an kafa wata kotu ta musamman, amma mutanen da yanzu suke zargina da sayar da su a kotun duniya suka bijire mata”.

Shekaru biyar da suka wuce ne dai zaben shugaban kasar da aka yi ta takaddama a kansa ya haddasa munanan hare-hare da hare-haren ramuwar gayya—an kona gidaje an kuma sassari mutane da adduna har sai da suka mutu da sunan kabilanci, yayinda ’yan sanda kuma suka mara baya ga wani bangare suka kuma yi amfani da karfin da ya wuce kima.

Wani muhimmin zargin da kotun ta duniya za ta bincika shi ne cewa manyan kasar ne suka bayar da umarnin aikata aika-aikar; kuma ma a fadar shugaban kasar aka yi wadansu tarurrukan sirri inda aka kitsa tashe-tashsn hankulan.

Image caption Firayim Ministan Kenya, Raila Odinga (daga dama) da Shugaba Mwai Kibaki

Yanzu haka dai wasu daga cikin matasan da aka diba su aikata aika-aikar sun yi batan dabo.

Jane Waruguru Mwangi ta bayyana cewa mijinta, Maina Diambo, ya yi ikirarin cewa ya halarci tarurrukan.

An yi ikrarin cewa an dauki hayar kungiyar ’yan daba ta mungiki, wadda Diambo ke jagoranta, don su kai hare-haren ramuwar gayya.

Wata rana dai an nemi Diambo an rasa kuma yanzu haka ana tunanin ya mutu.

Babbar mai shigar da kara ta kotun duniya Fatou Bensouda ta bayyana cewa lallai akwai yunkurin da ke yi na hurewa masu bayar da shaida kunne.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta yi gargadin cewa zaben da za a gudanar a wata mai zuwa a kasar ta Kenya ka iya karewa da tashe-tashen hankula.

Ta kara da cewa gwamnatin kasar ta kasa aiwatar da muhimman sauye-sauye da nufin magance musabbabin tashe-tashen hankulan.

Karin bayani