An kai harin kunar bakin wake a Mali

mali
Image caption An yi barin wuta da manyan makamai a Bamako

An yi ta barin wuta da manyan makamai a Bamako babban birnin kasar Mali tsakanin sojoji da kuma sojojin lema wadanda ke biyayya ga tsohon shugaban kasa Amadou Toumani Toure wanda aka hambarar a wani juyin mulki a bara.

An ce rikicin ya barke ne lokacin da sojojin suka nemi fitar sojojin lemar daga barikokinsu.

Sai dai an ruwaito cewa a yanzu kura ta lafa.

A halin da ake ciki kuma wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a kusa da garin Gao kuma soja daya daya ya sami rauni.

Sojojin da dakarun Faransa ke jagoranta suna ta fafatawa da yan tawayen Ansaruldeen a kusa da garin Gao wanda kafin lokacin baya bayan nan ya kasance garin da yan tawayen suke da karfi.

Karin bayani