'Faransa ta biya AQIM kudin fansa a 2010'

Vicki Huddleston
Image caption Tsohuwar jakadiyar Amurka a Mali, Vicki Huddleston

Wata tsohuwar jakadiyar Amurka a Mali ta ce Faransa ta biya kudin fansa don a sako mutanenta da aka yi garkuwa da su a shekarar 2010—kudin da suka kare a aljihun kungiyoyin masu tsattsauran ra'yin Musuluncin da yanzu take yaka a Mali.

A wata hira da ta yi da wani gidan talabijin na Faransa, tsohuwar jakadiyar, Vicki Huddleston, ta ce kasar ta Faransa ta biya dala miliyan goma sha bakwai don a sako mutanen da aka yi garkuwa da su a wata mahakar uranium da ke Nijar.

“Kusan shekaru biyu da suka gabata kungiyar Al-Qa'ida a Yankin Maghreb (AQIM) ta yi garkuwa da wadansu Faransawa a wata mahakar ma'adinai a arewacin Nijar. Don a saki wadannan mutane Faransa ta biya kudin fansa da ake zargin yawansu ya kai dala miliyan goma sha bakwai”, inji Ms Huddleston.

A cewarta, “Amma fa an san cewa ba zuwa Faransa kawai za ta yi ta ce ga kudinku ba—kamar sauran kudaden fansa da ake biya, wannan ma an biya ta hannun gwamnatin Mali kafin kudin, ko kuma wani bangare na kudin, ya kare a aljihun ’yan kungiyar ta al-Qa'ida”.

Tsohuwar jakadiyar ta kuma ce wadansu kasashen Turai ma, ciki har da Jamus, sun biya kudaden fansar da a jimilce suka kai kusan dala miliyan casa'in.

Faransa dai ta sha musanta cewa ta biya kudin fansa don a sako mutanen; amma Ms Huddelstone ta shaidawa BBC cewa an sako mutanen ne saboda wasu kudade sun gitta:

“Duk kasashen Turan da suka biya kudin fansa sun musanta biyan kudaden, kuma kamar yadda kuka sani mai yiwuwa suna musanatwa ne saboda kudaden sun bi ta hannu wadansu kafofi na gwamnatin Mali. Lokacin da nake Mali, ina da masaniya cewa Gwamnan Gao, wanda ya riga mu gidan gaskiya, yana cikin wadanda suka shiga daidaita tsakanin bangarorin biyu [dangane da kudin da za a biya]. Ai ba don tsabar kirkin da take da shi ba ne kungiyar AQIM ta saki mutanen”.

Karin bayani