An kashe masu allurar polio a Najeriya

Ana diga rigakafin Polio a Najeriya
Image caption Ana diga rigakafin Polio a Najeriya

Rahotanni daga birnin Kano a arewacin Najeriya na cewa da safiyar Juma'a wadansu 'yan bindiga a kan babur mai kafa uku—wanda ka fi sani da suna Keke NAPEP ko A Daidaita Sahu—sun kai hare-hare a kan jami'an kiwon lafiya masu riga-kafin kamuwa da cutar polio, wato shan inna.

An kai hare-haren ne a kan wasu dakunan shan magani da ke Filin Kashu a Unguwa Uku da kuma unguwar Hotoro Haye inda 'yan bindigar suka bude wuta.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce akalla masu allurar rigakafin tara ne 'yan bindigar suka kashe.

Kusan dukkan wadanda suka mutu mata ne, sai kuma namiji daya.

Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su amma suka tsira da ransu sun shaida wa wakilin BBC cewa maharan sun cinna wuta a wuraren da suka kai harin.

Wasu mallaman addinin musulunci a arewacin Najeriyar na nuna adawa da yin alluran rigakafin.

Najeriya, da Pakistan, da Afghanistan ne dai kasashe uku kacal a duniya inda har yanzu cutar ta polio ke bayyana.

Gidauniyar da ke yaki da cutar Polio a duniya ta ce an samu mutane 121 da suka kamu da cutar Polio a Najeriya a shekarar da ta gabata, idan aka kwatanta da 58 da aka samu a Pakistan da kuma 37 a Afghanistan.

A watan Disamban bara ma an kai wadansu hare-hare a kan jami'an kiwon lafiya masu allurar riga-kafin kamuwa da cutar ta polio an kuma kashe akalla takwas a kasar Pakistan.

Kungiyar Taliban na zargin kasar Amurka na amfani da ma'aikatan lafiyar da ke rigakafin Polio wajen yin leken asiri, sannan kuma in ji su, rigakafin ka iya hana yara haihuwa a nan gaba.

Karin bayani